LITTAFIN MUTUM KO ALJAN COMPLETE

MUTUM DA ALJAN Littafi Na Biyu (2) Part B. Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau Ke magana . KUMA YA DAGA KANSA YANA TUNANI har izuwa tsawon yan dakiku daga can sai ya dubi Yarima yayi murmushi yace yakai dana kayi sani cewa sama da shekaru goma baya na firgita gaba dayan makiyana ya zamana cewa sun razana dani ainun.Da yawansu na turmushe su na kau dasu daga doron kasa,wasunsu kuwa hijira sukayi suka bar kasashen su,suka bazama izuwa sassan duniya nesa da inda nake.Ina mai tabbatar maka da cewa na kashe sama da sarakai arba'in a wannan lokaci,don haka ina da tabbacin cewa babu sauran irin makiyana a wannan nahiya tamu gaba daya.Lokacin da sarki Alkasim yazo nan a zancensa sai ya bushe da dariyar mugunta yace haba yakai dana wai shin me kake shakka ne har yanzu?Yanzu kai a tunaninka har akwai wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda zaiyi gangancin farautar rayuwata alhalin yasan cewa nine GUGUWAR ANNOBA mai baje birane kuma nine KOGIN JINI mai shanye ALKARYA.Sa'adda yarima Kamsus yaji wannan batu na mahaifinsa sai yayi ajiyar zuciya yace yakai Abbana ka yi sani cewa wannan duniya tana da fadi,haka kuma abubuwan cikinta yawa garesu kuma komai nisan gari akwai wani a gabansa.Tabbas na yarda cewa kai ZARTO ne abin tsoro kuma kai tauraro ne wanda ya haska duniya amma ka sani cewa ZAMANI RIGA CE.Dole ne mai laya ya kiyayi MAI ZAMANI.Kullum shekarunka tafiya sukeyi kuma kullum ana samun sauyin al'amara na cigaba.A halin yanzu a iya binciken da nayi na gano cewa akwai makiyanka a cikin wannan tawaga tamu,amma gashi ni da kai da dukkan dakarunmu mun kasa gano ko su waye wadannan makiya.Asalima mun kasa ganinsu a zahiri.Shin ba zaka iya tuno da makiyanka na karshe ba wadanda baka sami nasarar kawar dasu ba ko kuma akwai wadanda kake zargin cewa nan gaba zasu iya zama makiyanka?Koda sarki Alkasim yaji wannan tambaya sai yayi shiru kuma ya nutsu sosai,nan take ya fada cikin kogin tunani bisa abinda ya faru a baya.Bayan ya gama tunanin ne ya dubi yarima Kamsus yace shin zaka iya tunowa da al'amarin daya faru a birninmu kimanin shekaru bakwai baya sa'adda baka fi shekara goma sha daya ba a duniya?Koda jin wannan tambaya sai zuciyar yarima Kamsus ta buga da karfi.Sarki Alkasim ya cigaba da cewa akwai watarana da wani bakon boka ya sauka a birnin ya gurbata ruwan shanmu,na kafa doka mai tsauri akan duk mutumin daya sake bata mana ruwan sha Hukuncin kisa ne a kansa.Bayan shekara guda da faruwar al'amarin ne wani bakon bafatake tare da matarsa da 'ya'yansa guda biyu tagwaye suka zo suka sake gurbata mana wannan ruwan sha namu.Koda aka gurfanar dasu a gabana sai nan take na yankewa mutumin hukuncin kisa ba tare da nayi bincike naji dalilin laifinsa ba.Wannan shine kuskure na guda daya jal a rayuwata wanda har kwanan gobe nake yin nadamar aikatashi saboda nayi amfani da karfin mulkina ne don tsorata masu kawo wargi na tafka zalunci saboda wannan bakon bafatake ba'a kan laifi na hukunta shi ba.Yayi laifin ne bisa tsautsayi da rashin sani.A iya tunani yayan wannan bafatake zasu iya girma su zama abokan gabata tunda a gaban idanunsu nasa aka kashe mahaifin nasu suna kuka da ihu suna rokona gafara.Bazan taba mantawa ba a sannan saida kai ma ka roke ni akan nayiwa mahaifin nasu afuwa.Koda sarki Alkasim yazo daidai nan a labarinsa sai nan take yarima Kamsus ya tuno da lokacin da Jaruma Namrita ta waigo tana kallonsa,sa'adda mahaifiyarsu ta janyesu ita da dan uwanta lokacin da suke ficewa daga cikin birnin misra.Nan take Kamsus ya gane cewa wadannan idanu daya gani a shekaru bakwai baya sune ya sake gani a yanzu akan fuskar wannan macen tagwayen.Kawai sai hawaye ya zubowa yarima Kamsus ya dubi sarki Alkasim cikin alamun karayar zuciya yace tabbas wadanann yayan bafatake sune ke biye damu a cikin wannan tafiya tamu domin su dauki fansa a kanka kuma ina ji a jikina cewa suna nan a kusa kuma a koyaushe zasu iya kawo harin bazato.Koda jin wannan batu sai sarki Alkasim ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya ta mugunta.Al'amarin daya firgita gaba dayan jama'ar dake sansanin kenan har shugaban dakaru da sauran yaransa suka rugo da gudu izuwa gaban tantin sarki.Koda ganin haka sai sarki ya mike tsaye ya fito daga cikin tantin ya dubi shugaban dakaru Uzaila bin Kaidas yace dashi maza ka janye gaba dayan yaranka daga cikin sansanin nan da wajensa bana bukatar daya daga cikinku ya sake bani tsaro har sai na sake bukatarku da kaina.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma musamman na yarima Kamsus don haka sai ya dubi sarki cikin alamun matukar kaduwa gami da firgici yace haba ya Abbana ai wannan ba karamin ganganci bane kayi tamkar ka siyar da rayuwarka ne ga makiyanka.Sarki Alkasim ya dafa kafadar yarima yana maiyin murmushi a gareshi yace yau ne zan nuna maka cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane,kuma ni MURUCIN KAN DUTSE ne ban fito ba saida na shirya.Karo dani sai DUBU TA TARU.Wadannan tagwaye guda biyu na dade da saninsu kuma nasan da zuwansu kasata a wannan lokaci.Macen Sunanta Namrita shi kuma namijin sunansa Zaihas.Saida suka shekara bakwai suna yawo a duniya suna ziyartar manyan bokaye da manyan jarumai suna koyon fada,yaki da tsafi ba don komai ba sai domin su sami nasarar daukar fansa a kaina.A yanzu haka suna can gaba kadan cikin wani daji mai DUHUWA wanda ake kira SURFAL wanda tazararmu dashi bata wuce zira'i arba'in ba.A yau din nan idan dare ya raba zasu kawo mini harin bazato domin su hallaka ni don haka nake son kowa ya kauce daga kan hanyarsu banda yarima domin mu biyu ne kacal zamu iya tsira daga sharrinsu.Sa'adda sarki Alkasim yazo nan a... ★Abubakar Haleefah Physicist★ Jawabinsa sai Uzaila ya risina yace an gama ya shugabana.Nan take shugaban dakaru Uzaila ya tattaro gaba dayan dakarun sarki ya tafi dasu izuwa can gaban sansanin suka kafa nasu sansanin.Suma ragowar gaba dayan abokan tafiyar sai suka bi su Uzaila ya zamana cewa saura sarki da yarima Kamsus kadai a cikin sansanin suna kallon juna.Shidai Yarima Kamsus tsananin mamaki ne yasashi yayi shiru kawai yana mai kurawa sarki Idanu domin ya firgita da al'amarinsa,bai taba zaton cewa yasan komai ba haka akan wadannan makiya nasu.Kawai sai sarki ya dubi Yarima yace kai kuma me ka tsaya kake jira!Ai sai kabi sauran jama'ar kaima so nake a barni ni kadai.Koda jin haka sai Yarima Kamsus yayi wuf ya durkusa bisa guiwoyinsa ya kama kafar sarki yace ina mai rokonka daka barni naga yadda zata wakana tsakaninka da wadannan abokan gaba.Koda jin haka sai sarki yayi shiru yana tunani sannan yace shi kenan na amince zan barka ka tsaya tare dani amma bisa sharadi biyu.Kada ka tayani yakar wadannan makiya nawa kuma kada ka karesu.Sa'adda Yarima Kamsus yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun amma saiya kudurce a cikin ransa cewa saiya zartar da abinda ke cikin ransa koda ransa zai baci daga baya don haka sai ya dubi sarki cikin murmushi yace na amince da wannan sharadi naka.Lokacin da dare ya raba sai dajin gaba daya yayi tsit,ba'a jin sautin komai face na kadawar iska gami da kukan kananan kwari da tsuntsaye.A wannan lokaci tuni sarki Alkasim ya dade da fara yin bacci harda munshari abinsa,shi kuwa Yarima Kamsus yana zaune a gefe daya cikin tantin ya kurawa sarki Idanu kawai yana mamakinsa yana mai cewa a cikin ransa waishin sarki wane irin hatsabibin mutum ne shi haka?Yaya shi da yasan cewa za'a zo kashe a cikin wannan dare amma kuma saiya kwanta ya kama bacci abinsa ba tare da fargabar komai ba?Gama fadin hakan keda wuya sai kawai yaji saman tantin nasu ya dare gida biyu.Kafin ya daga kansa sama yaga abinda ke shirin faruwa tuni Jaruma Namrita da Jarumi Zaihas sun duro cikin tantin sun kaiwa sarki Alkasim suka a ciki da takubbansu.Cikin bakin zafin nama sarki Alkasim ya doki kasa da tafin hannayensa yayi sama tamkar da majajjawa aka janyeshi,sai takubban nasu suka soke a cikin kasa suka lume.Kafin su zaro takubban tuni sarki ya tale kafafunsa a sama ya doki kirazansu.Duk da karfin dukan kirjin nasu da yayi basu fadi kasa ba amma saida sukayi baya,nanfa aka kacame da azababben yaki mai tsananin ban tsoro da al'ajabi.Duk wannan abu dake faruwa Yarima Kamsus na zaune a inda yake ko motsawa baiyi ba kawai ya zubawa JARUMAN UKU idanu yana kallon masifaffen yakin da sukeyi na ban al'ajabi da ban tsoro.Saida aka shafe kusan rabin sa'a anayin wannan BAKIN ARTABU ba tare da tagwayen biyu sun sami nasarar koda kwarzanar jikin sarki Alkasim ba kuma tunda ka fara gumurzun sarki Alkasim bai mayar da martani ba kawai kare kansa yakeyi fuskarsa cike da murmushi tamkar wasa yakeyi ba yaki ba.Ashe so yake kawai ya fahimci iyakar jarumtakar wadannan tagwaye.Koda yaga tagwayen biyu sun kasa yi masa komai saiya daka tsalle sama ya luluka sama yana katantanwa tamkar an murza dan mazari,shi kansa yarima Kamsus bai taba ganin irin wannan jarumtaka ba don haka bai san sa'adda ya daga kansa sama ba yana kallon IKON ALLAH.Suma tagwayen biyu haka suka daga kawunansu sama suna mamaki.Koda sukaga sarki Alkasim ya cigaba da lulukawa sama yana neman kulewa a cikin gajimare sai suka dubi junansu nan take sukayi amfani da karfin sihirinsu na tsafi suma suka tashi sama kamar tsuntsaye suka bi bayan sarki Alkasim da nufin su cimmasa.Kwatsam ba zato ba tsammani sai ganin sarki Alkasim sukayi daf dasu tamkar zukoshi akayi.Kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni sarki Alkasim ya gabza musu wawan naushi akan kirazansu saboda karfin naushin sai suka rikito kasa suna aman jini duk su biyun suka fado kasa tim suka baje a cikin wani irin mugun hali mai kama da suma sun jirkitar hankali.Kawai sai sarki Alkasim ya nufosu daga saman yana mai saito cikin kowannensu da tsanin makami zai soke su.Koda Yarima Kamsus ya kyallara idanu yayi arba da fuskar macen tagwayen a wannan lokaci yaga irin tsananin kyawun da Allah ya bata wanda bai taba ganin irinsa ba kuma yaga cewa tabbas sarki kasheta zaiyi kuma ya kashe dan uwanta sai ya zabura cikin bakin zafin nama ya janyesu daga inda suke kwance tamkar shaho ya suri yan tsaki yayi jifa dasu izuwa cikin wata korama dake can gefe daya.Ai kuwa sai Sarki Alkasim ya soki kasa da makaman nasa maimakon ya sami nasarar soke cikinsu.Koda Namrita da Zaihas suka fada cikin wannan fadama ruwa ya jikasu sai nan da nan suka farfado daga suman da sukayi suna bude idanuwansu sai suka hango sarki Alkasim ya nufo su da gudu a sama tamkar ya kasance kibiyar da aka harbo daga cikin baka saboda karfin gudun nasa.Saura baifi taku uku ba kacal ya sake samun nasarar soke su sai yaga sun daidance sun zama kamar kwayar zarra sun shige cikin karkashin kasa sun bace bat. AA Misau ke magana

Comments