LITTAFIN GIDAN UNCLE COMPLETE..
Gidan Uncle Page OneZaune suke a dinning table gaba daya ahlin gdan guda biyar suna dinner cike da kulawa da tattalin juna yarane guda biyu mata kyawawa sai wata yar matashiyar budurwa da bazata wucce 17 years kyakkyawa ce sosai Mai dirarren jiki duk da a zaune take da alamun bazata cika tsayi ba kuma ba gajeriya bace ba fara bace tass kuma ba baqa ba itadai zaa iya kiranta wankan tarwada tanada murjajjen jiki sosai kuma tanada cikar halitta sosai.Yar matashiyar matar gdan da itama bazata wucce 25 years ba ta kalleta tace “Hameed kamar wani Abu yana damun qanwarka Umaimah fah naga kwana biyu bata da walwala sosai ko kai baka lura da hakan ba?” ajiye cokalin hanunsa yayi dago ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace “bazai wucce tunanin Ummanki ba ko?” Saurin daga masa kai tayi tace “wlh Uncle narasa meyasa duk tsayin shekarun nan da na rasa mahaifana bantabajin ciwon rashinsu ba sai a yan kwanakin nan…”Tayi shiru da mgnr saboda kukan da yakecin zuciyarta yan qananun yaran g...