ANA WATA GA WATA: Rarara Ya Shiga Tangal-tangal Ɗin Wasan Ƴar Ɓuya Da Jami'an Kotu Kan Bashi Sammacin Tuhumar Sama Da Naira Miliyan Goma An gurfanar da shahararren mawaƙin jam'iyar APCn nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), a gaban babbar kotun shari'ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Rijiyar Zaki Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Halhaltul Khuza'i Zakariya. Tun da fari wani mai suna Muhammad Ma'aji ne ya maka Rarara a gaban kotun kan wasu kuɗaɗen sa Naira Miliyan ₦10.3m da suka ƙulla wata harka a watannin da suka gabata. Mai ƙarar ya shaida wa kotun cewa, bashi da wani zaɓi dan ya ƙarɓi haƙƙinsa sai ta fannin shari'a kamar yadda kowa yake da ƴan cin shigar da ƙara kan hanashi haƙƙinsa. Muhammad Ma'aji ya ƙara da cewa ya bi matakin sulhu da wanda yake ƙara dan ya bashi kuɗin sa tunda dai harkar bata yiwu ba kuma yaƙi bashi kuɗinsa. Kakakin manyan kotunan shari'ar Addinin musulinci na jahar Kano Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa...